Shahararran marubuci Datti Assalafy ya yiwa Jaruma Maryam Yahaya martani akan wasu sabbin hotuna data wallafa
Shahararran marubuci Datti Assalafy yayi magana akan wasu sabbin hotunan da Jarumar Masana’antar Kannywood Maryam Yahaya ta wallafa, bayan ta sami saukin rashin lafiyar data sha fama da ita.
Kamar yadda kuka sani a kwanakin baya Jaruma Maryam Yahaya ta kwanta rashin lafiyar data sha wahala sosai wanda har kamanninta suka saura.
Bayan Jarumar ta fara samin saukin rashin lafiyar dake damunta sai ta fara wallafa hotuna a shafinta na sada zumunta Instagram, wanda har Jama’a suka fara cece-kuce a kan hotunan.
To a yanzu ma Jaruma Maryam Yahaya ta wallafa wasu hotuna wanda shahararran marubucin nan Datti Assalafy yayi magana akan su, inda yake fadin cewa.
Maryam Yahaya an bata shawara ta killace kanta ta dena yada hotunanta a media ta bari sai ta murmure amma taki.
Nayi magana da daya daga cikin uwayen dakinta a Masana’antar Hausa film ta tabbatar min da cewa yarinyar bata karban shawara.
A cikin wannan yanayi da take ciki abar a tausaya mata ne, Allah kadai ya san wa take son ta burge kuma a media, na san dai ba zata taba burge wadanda suka zalunceta ba domin sun gujeta.
Muna bata shawara ta sanya Hijabi idan zata yada hotonta a media, zaifi rufa mata asirin ramar da tayi sakamakon jinyar Typhoid da yake damunta a cewarta.
Ga hotunan da Jaruma Maryam Yahaya ta wallafa a kasa wanda Shahararran marubuci Datti Assalafy yayi magana akan su.
cialis 20mg ca purchase tadalafil without prescription causes of erectile dysfunction