Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Tsohuwar Matar Jarumi Adam a zango Amina Uba Hassan ta bayyana ra’ayin ta na dawowa harkar Fim a yanzu bayan auren su ya mutu

Jarumar Masana’antar shirya Fina-Finan Hausa ta Kannywood Amina Uba Hassan wacce ta kasance tsohuwar Matar Jarumi Adam a zango, a wannan lokacin ta dawo Masana’anyar Kannywood domin ta cigaba da harkar Fim.

Advertising

Amina wacce aka fi sani da Maman Haidar ta fara harkar Fim ne a Kannywood shekarar 2000 bayan nan kuma sai ta auri Jarumi Adam a zango a shekarar 2007, kamar yadda Jaridar Damukaradiyya ta ruwaito.

Bayan auren nasu da Jarumi Adam a zango Amina Uba Hassan ta haifi dan ta Namiji a shekarar 2008, bayan haihuwar ta ne kuma sai auren nata ya sami tangar da bayan wasu watanni biyar 5.

Jaruma Amina Uba Hassan ta bayyana a wani shirin Fim mai suna “Gidan Danja” wanda kamfanin 2Effects ya shirya a kwanakin baya da suka gabata.

Advertising

Sannan Jarumar wacce ta kasance ‘Yar asalin Jihar Kaduna ta bayyana cewa, ta dawo Masana’antar Kannywood ne domin cigaba da harkar Fim fiye da yadda ta bari a baya, kuma a wannan karon sararin sama ne iyakar ta.

Amina Uba Hassan ta sake bayyana cewa: Yana da wahala sosai a matsayin ta na wacce ta haihuwa kuma bazawara ta sake komawa industry bayan barinsa na fiye da shekaru 10, zai da na tuntubi mutane da dama tare da juriya kafin na yanke shawarar. Babu shakka, yin fina-finai shine abin da na ke kaunar yi don haka zan cigaba da yi.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button