Wani Malamin addini ya kawo addu’ar neman tsari daga masu garkuwa da Mutane a Nageriya
Har yanzu dai maganganu basu kare ba akan ta’addancin dake faruwa a Arewacin Nageriya inda Malamai da sauran a’umma suke suke aika sakonni ga Shugabanni domin neman mafita kan abubuwan da suke faruwa.
To a yanzu kuma sun sami wata bidiyo daga Tashar wanda Tashar Kundin shahara dake kan manhajar Youtube ta wallafa.
Inda a cikin bidiyon mukaga wani Malamin addini yana bawa al’umma shawara akan cewa, ya kamata suna neman addu’o’in kare kai kodan irin abubuwan da suke faruwa a halin yanzu.
Malamin yayi cikekken bayani tare da shawurtar al’umma akan gudun mawar addu’o’in da yake badawa domin ayi amfani da su wajan kare kai.
Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji cikekken bayani daga bakin Malamin, da kuma irin addu’o’in da yake fadawa al’umma domin suyi amfani da su wajan kare kan su.
Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla.