Ana kira tare da gargadi akan Malaman Nageriya da Sarakuna dasu kame bakin su akan wasu maganganu da suke fada
ANA GARGADIN MALAMAI DA SARAKUNA
SU KAME BAKINSU.
Wannan mutumi da ake gani sunansa Peter Afunanya, shine yake magana da yawun hukumar jami’an tsaron farin kaya DSS.
Mista Peter Afunanya ya fitar da sanarwa yana gargadin Malaman addini da Sarakunan gargajiya da sauran jama’a akan su rufe bakinsu daga yin magana akan abinda ya shafi tsaro wanda zai kawo fitina a Cikin kasa.
Afunanya yace hukumar DSS ta fahimci akwai wasu ‘yan siyasa da suke neman mulki ido a rufe, suna amfani da hanyoyin da basu dace ba wajen siyasantar da lamarin tsaro wanda zai tunzura al’umma.
Wallahi a raina nasan za’a kawo wannan matakin da za’a tsoratar da Malamai wanda muryoyinsu ka kaiwa, kwanaki kadan da suka wuce DSS reshen Jihar Sokoto sai dat gayyaci Sheikh Bello Yabo Sokoto ta tuhume shi akan maganganun da yayi wanda ya shafi batun cire tallafin man fetur da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari take yunkurin cirewa.
Magana ta gaskiya duk Malamin da bai da daurin gindi kuma bai da kudin daukan manyan lauyoyi, to ya san maganar da zai furta hatta manyan ‘Yan Social media da sakonnin mu yake girgiza tebur sai mu shiga taitayin mu.
Wannan ita ce Nigeria da muke rayuwa yau a cikinta a dakemu sannan a hanamu kuka dadin abin babu wanda zai tabbata akan wata kujera na mulki ko aiki.
Akwai ranar sauka da kuma ranar ritaya za’a dawo cikin al’umma a cigaba da rayuwa da su cikin rashin tsaro, muna rokon Allah Ya isar mana a inda akafi karfin mu.