Datti Assalafy yayi shira da Malamin addini Sheikh Bello Yabo akan masu yada fastar sa da cewa zai fito takarar Gwaman Jihar Sokoto
Idan baku manta ba a kwana baya anyi ta wallafa fastar Shahararran Malamin addini Sheikh Bello Yabo dake Jihar Sokoto, inda ake cewa wai Malamin zai fito takarar Gwamnan Jihar Sokoto a karkashin Jam’iyyar (PDP).
Inda nan take Shahararran marubucin nan Datti Assalafy ya bayyana wani rahoto game da zantawar da sukayi da Sheikh Bello Yabo Sokoto.
Ga zantawar da suka yi da Sheikh Bello Yabo Sokoto.
Lokacin da naci karo da wannan fosta mai dauke da hoton Babban Malamin Musulunci dodon azzaluman shugabannin Nigeria Sheikh Bello Yabo Sokoto cewa, Malam zai fito takarar Gwamnan Jihar Sokoto a 2023, nayi matukar murna da farin ciki duk da naji a zuciyana ba daga gareshi ba ne.
Amma nan take na dauki wayata na kira Sheikh Bello Yabo Sokoto bai dauka ba, bayan kamar awa biyu sai ga kiransa ya shigo wayata, bana kusa da wayan matata ta miko min tace ga Malam Bello Yabo na kira.
Da amsa kiran waya muka gaisa da Malam sosai ya kama sunana muka yiwa juna jaje akan matsalar tsaron da yake faruwa, daga nan sai na tambayi Malam game da fostansa da na gani sai Malam yace min kamar yadda na gani a media shima haka ya gani, bai da masaniya a kai muka dan zanta da Malam kan matsalar tsaro daga karshe ya sa min albarka mukayi Sallama.
Tun farko na san cewa wasu ne kawai suka kirkiri wannan fosta, amma har ga Allah na ji dadin ganin haka, kuma har zuwa yanzu ina fatan ace hakan ya tabbata.
Dole Malamai su tashi su shiga siyasa su kwace iko da ragamar Gwamnati manyan ‘yan Demokaradiyyah ba wa’azi suke saurara ba, basu da lokacin sauraran wa’azin Malamai balle su fahimci hakkin Allah da al’umma a kansu sunfi saurara bokaye da ‘yan kungiyar asiri.
Da zaku samu access da wayoyin ‘yan siyasar da suke wakiltarmu ku duba wayoyinsu ba zaku tarar da wa’azi ko guda daya a ciki ba, sai wakokin banza da hotunan karuwai, ku dubi kafofin sada zumunta na ‘yan siyasarmu, basa fallowing din duk wani shafi da ake wa’azi, sam basa sauraran wa’azi.
Suna amfani da Malamai ne domin su cimma burinsu na siyasa kadai idan wani Malami ya tashi zai fada musu gaskiya sai su kwabe bakinsa, yanzu ba gashi nan ba wai DSS tana gargadin Malamai da Sarakuna su dena magana akan tsaro, yau inda shugaban kasa Malami ne DSS ta fito ta gargadi Malamai ai zai sauke shugaban DSS din daga mukaminsa saboda rainin wayo ne wannan da kuma cin fuska.
Miyagun ‘yan siyasa sun dauki Malamai a matsayin wasu karnukan farauta ne kawai wadanda ake amfani dasu wajen neman kuri’ah, da zaran anci zabe ko mukamin PA ba za’a bawa Malami ba ashe ya kamata Malamai su shiga siyasa su kwato ‘yancinsu da na al’umma.
Idan ana batun Musulunci da neman mafita ba’a kawo batun banbancin akida, misali a matsayina na Datti Assalafiy Basalafe dan kungiyar Izala idan aka tsayar da wani babban Malami na darikar Tijjaniyyah ko Qadiriyya kamar Professor Sheikh Ibrahim Maqari, takaran shugaban kasa da Muhammadu Buhari, Wallahi zan ajiye Muhammadu Buhari a gefe na zabi Malami irin Maqari ya zama shugabana.
Mun yadda siyasar Nigeria a gurbace take saboda gurbatattun mutane ne ke jan ragamarta, don haka ya kamata Malamai mutanen kirki su kwace ikon kasar.
Tun farkon duniya Shugabanci na Malamai ne Malamai sune magada Annabawan Allah wanda suka shugabanci duniya, babu masu gyara gurbatacciyar kasa irin Nigeria Wallahi sai Malamai da suka karantu a addini da boko.
Shekarar 2023 na tafe ya kamata jama’ar Musulmin Arewa gaba daya a hadu a tsayar da Malamai takara a gujeran Shuaban kasa, Gwamna, Sanata da ‘yan majalisu, da hakane Musulmin Arewa zasu samarwa kansu cikakken ‘yanci da magance matsalolin tsaron dake addabar mu.
Muna rokon Allah Ya canza mana miyagun shugabanni, Ya maye mana gurbinsu da mutanen kwarai ba don halin mu ba.