Labaran Kannywood

Ficaccan Mawakin Siyasa Dauda Kahutu Rarara ya baiwa Mawaki Abdul D One tare da Amaryar sa kyautar sabbin Motoci guda 2

Kamar yadda kuka sani a shekaran jiya ne aka gudanar da shagalin bikin Ficaccan Jarumin Masana’antar Kannywood, Abdul D One tare da Amaryar sa Salma Fresh.

To a yau kuma munci karo da wani labarin abin farin ciki wanda Shahararran Mawakin Siyasa kuma Dan cikin Masana’antar Kannywood Dauda Kahutu Rarara, ya baiwa Mawaki Abdul D One tare da Amaryar sa kyautar sabbin Motoci guda biyu.

Mai magana da yawun Dauda Kahutu Rarara shi ya wallafa wannan labarin abin farin cikin a shafin sa na sada zumunta Instagram, inda yayi wallafar kamar haka.

𝐑𝐀𝐑𝐀𝐑𝐀 π˜π€ 𝐆𝐖𝐀𝐍𝐆𝐖𝐀𝐉𝐄 π€ππ†πŽ 𝐃𝐀 π€πŒπ€π‘π˜π€ 𝐃𝐀 πŠπ˜π€π”π“π€π‘ πŒπŽπ“π€ 𝐀 𝐑𝐀𝐍𝐀𝐑 𝐀𝐔𝐑𝐄𝐍 𝐒𝐔.

Chairman Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara Ya Gwangwaje Ango Abdul D. One da Amaryarsa Salma Sulaiman da Kyautar Mota Kirar Honda EOD a Ranar Auren Su, Chairman Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara Yayi Musu Fatan Allah Ya Sanya Al-Kairi Tare da Addu’ar Allah Ya Basu Zaman Lafiya.

Motoci Takwas da Babur Daya Kenan Ango da Amarya Nima Ina Tayaku Murna.

Rabi’u Garba Gaya Media Aide to Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara APC Director General Campaign Musics.

Inda shima mawakin abdul d one yayi godiya ga Rarara kamar haka.

Me Gidan Mu Kuma Dan Uwan Mu Kullum Cikin Wasa Da Dariya Muke Rabuwa Ngde Da Wannan Babbar Kyauta Kasani Farin Ciki A Ranar Farin Ciki Allah Yasaka Farin Ciki Har Abada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button