Har yanzu dai Jarumin Kannywood kuma Darakta Falalu a Dorayi ya sake yin martani akan matsalar tsaron Arewa
Kamar yadda kuka sani Falalu a Dorayi Ficaccan Jarumi ne a Masana’antar Kannywood sannan kuma Darakta wanda ya shirya Shirin nan mai dogon zango wato “Gidan Badamasi”.
A yau ne Jarumi Falalu a Dorayi ya wata wallafa a shafin sa na sada zumunta Instagram akan abubuwan da suke faruwa a Kasar Nageriya Musamman Arewacin Kasar.
Inda Falalu a Dorayi ta wallafa wani dan gajeren rubutu kamar haka.
Wai a Haka aka cewa za’a Kare rayuka a can cikin Daji manyan ‘Yan ta’adda dauke da bindugun yaki na gaske.
Wani gefan kuma An zabe karfafa daga cikin Jami’an tsaramu, masu rike da ingantattun makamai suna Gadin Iaflyar mara kishin mu cikin Shugabanni da iyalan su.
Yayin da wasu Jami’an tsaronmu ke kukan da karancin makamai.
Abin takaici wai wanda zai kare al’umma ne rike da tsohuwar bindiga Kamar ta yakin duniya na daya, Ko kaga wasu da kulki sai ka ce dogarai, dole ‘Yan ta’adda
suyi barna Iokacin da suka ga dama. Katin zabenka makamin ka.
In sha Allah da shi za’a tura duk wani marar kishin Arewa ya zauna a gida.