Innalillahi wa inna ilaishi raji’un: Allah ya yiwa Jarumin Masana’antar Kannywood Sani Garba SK Rasuwa
Innalillahi wa’inna ilaihi raji’um: Ficaccan Jarumin Masana’antar Kannywood Sani Garba SK Allah ya yi masa rasuwa a yau Talata.
Mun sami wannan wallafar labarin ne daga shafin BBC Hausa dake kan Instagram, inda suka wallafa labarin kamar haka.
Ficaccan Dan wasan Hausa Sani Garba SK ya rasu a Kano bayan fama da doguwar jinya a asibitin Nasarawa a yau Laraba.
Idan baku manta ba a kwanakin baya an sha wallafa labarin cewa, Jarumi Sani Garba SK ya rasu amma daga baya sai jarumin ya bayyana a cikin wata bidiyo inda yake bayani kan cewa, shi bai rasu ba sannan kuma ai mutuwa dole ce kuma tana kan kowa.
To a yau kuma Allah ya yiwa Jarumin rasuwa, muna rokon Allah yaji kan sa ya gafarta masa yasa aljanna ce makomar sa, mu kuma idan tamu tazo Allah yasa mucika da imani, Ameen.