Labarai
Shugaban kasa Muhammad Buhari yana iya bakin kokarin sa kan matsalar tsaro a Nageriya, cewar Sheikh Bala Lau
Buhari Na Bakin Kokarinsa Kan Matsalar Tsaro. Cewar Shaikh Bala Lau. Daga Indabawa Aliyu Imam.
Shugaban hadaddiyar kungiyar Izala ta kasa Shaikh Bala Lau ya bayyana cewa: komawa ga Allah ne kadai zai magance matsalolin tsaro, wanda suka ki ci suka ki cinyewa a Najeriya.
Malam Bala Lau ya kara da cewa: Alkunutu ne kadai mafita shi dama ana yi ne sanda bala’i ko musiba ya sami al’umma, ana so a yi addu’a a kaskantar da kai domin Allah ya shigo ciki.
A tattaunawar da sukayi da BBC Hausa Malamin ya kara da cewa: Gwamnati na bakin kokarinta sai dai ba zata iya ita kadai ba.