Advertising
Advertising
Labarai

Wace riba zaku samu idan kunci mutuncin Malam Isah Ali Pantami shidin fa garkuwa ne ga Musulinci da kuma Arewa, Daga Datti Dattifi

MALAM ISA ALI PANAMI GARKUWA NE Ga MUSULUNCI DA AREWA. Daga Datti Dattiļ¬.

Advertising

Datti Dattifi ya fara da cewa: Yaushe wace rana Sheikh Professor Dr Isa Ali Pantami ya zama Ministan tsaron Nigeria, Ya kamata mai hankali ya kalubalanci Malam akan matsalar tsaro.

Ministan tsaro dan Jihar Kano ne sunan sa Bashir Salihi Magashi, me yasa bakwa cin mutuncin sa akan rashin tsaro sai Malam Isa Ali Pantami ministan Sadarwa.

Ya kara da cewa: Masu cin mutuncin Malam sun ce kafin Malam ya shiga Gwamnati yana kalubalantar shugabanni akan mumbari, ku sani cewa a lokacin bai da wata hanyar isar da sako garesu imba mumbari ba, yanzu kuma yana.

Advertising

Cikin Gwamnati yana rike da mukamin Ministan Sadarwa duk da haka yana bada shawara akan abinda ya shafi tsaro, kuma yana isar da sakon ‘yan Arewa da Musulunci A kaf cikin Ministocin shugaba Buhari babu.

Minstan da ya kai Malam aiki a ma’aikatarsa lokacin annobar Coronavirus shi ya kubutar da Nigeria daga karayan tattalin arziki, ya kawo wa yankin Arewa babba cugaba ya gina cibiyoyi na koyar da ilmin na’ura mai kwakwalwa har a makarantun addinin Musulunci sai da ya kai ICT centers.

Ko da Malam yayi kuskure a baya shin ba zamu duba alherinsa ba, da shigar sa Gwamnati da rashin shigar sa
wannan yafi alheri.

Shin wadannan miyagun ‘yan Siyasar Demokaradiyyah suna jin wa’azin Malamai ne, idan ma Malami ya takura musu kamashi zasu yi ko su sa a hallakashi, don haka Malamai su shiga Gwamnatin su rike madafun iko zaifi
zama alheri.

Wani riba zaku samu idan kunci Mutuncin Malam Isa Ali Pantami kun bata masa suna, shin muna da irinsa a cikin Ministocin shugaba Buhari.

Ku sani cewa: Wallahi babu masu kawo gyarada canji akan matsalolin Arewa imba Malamai ba so muke Malamai su shiga cikin siyasa su kwace ikon shugabanci daga hannun jahilai azzalumai, ko ba komai Malami yafi kusa da jin tsoron Allah sama da katon jahili Dan boko zalla.

Mutane masu hankali da adalci suna duba alherin mutum ne ba kuskure ba alherin wannan bawan Allah Ya ninka kuskuren sa, ku kasance masu duba alherin sa ba kuskure ba Ina da dalilai wanda ko a gaban Allah ne zan iya kare kaina akan cewa Malam Isa Ali Pantami garkuwa ne a Arewa da Musulunci.

A cikin wannan Gwamnatin abubuwa da yawa suna faruwa wanda ake shiryawa Arewa manakisa yana kokari wajen toshewa Kamar yadda shigar Malam Isa Ali Pantami Gwamnati.

Bai hanashi karantar da addinin Musulunci ba to haka shigarsa Gwamnati bai hanashi kokarin kare martaban Arewa da Musulunci ba, Allah Ya zama shaida haka.

Muna rokon Allah Ya yadda da Malam Isa Ali Pantami tare damu, Allah Ya kara masa hakuri da juriya da girma da daukaka a idon makiyan sa da mahassadan sa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button