Ku gaggauta yin katin zabe domin kada a zaba mumu shugaba wanda bai cancanta ba, cewar tsohon Sarkin Kano Sunusi Lamido Sunusi
Ku Gaggauta Yin Katin Zabe, Sakon Tsohon
Sarkin Kano Ga Al’umma. Daga Indabawa Aliyu Imam.
Mai alfarma Sarkin Kano na goma sha hudu kuma Khalifan Tijjaniyya Sunusi Lamido Sunusi, ya bukaci al’umma da su gaggauta yankar katin zabe.
Mai martaba Sunusi wanda malamin addinin musulunci ne ya yi wannan bayani a karatun littafin Madarijus Saliki wanda yake gabatarwa a kowanne Mako.
Ana nan ana yin katin zabe don haka jama’a kowa ya mallaki nasa idan ba ku yi katin zabe ba aka za’ba muku shugaba wanda bai cancanta ba, to sai dai ku yi hakuri ba yadda zaku yi.
Amma kai ma kana da hakki ka jefa kuri’a don ka sami shugaban da kake so, don haka muna kira ga kowa ya mallaki katin zabe a cewar tsohon Sarki Malam Sunusi na biyu.
Sai dai masu sharhi da fashin baki na ganin akwai kwakkwarar alakar wannan magana ta Maimartaba tsohon Sarki kan rikicin sa da Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.