Advertising
Advertising
Labarai

Masha Allah: Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero zai Angwance da tsohuwar Budurwar sa

Masha Allah: Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero zai Angwance da tsohuwar Budurwar sa

Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yana shirin angwancewa da tsohuwar Budurwar sa wadda ake kira da suna Hajiyayye dake garin Dorayi a Kano.

Advertising

Sarkin Alhaji Aminu Bayero wanda matarsa daya da ‘Yayan sa hudu zai yi auren ne bayan tsahon lokaci yana zaune da mace daya.

Jaridar Daily Nigerian ta bayyana cewa: majiyarta ta bayyana mata cewar tuni shiri yayi nisa don tattaunawa da waliyyan tsohuwar Budurwar tasa don sanya lokacin auren.

Advertising

Majiyar ta kara da cewa: An sha daga lokacin auren sakamakon an shirya gudanar dashi ba tare da shirya bukukuwa irin na al’ada idan za’a yi aure a gidan sarauta ba.

Kamar yadda majiyar ta bayyana cewa: Mai martaba Sarki Alhaji Ado Bayero ya dade tare da Hajiyayye tun kafin ya zama Sarki.

An haifi Sarki Aminu Ado Bayero a shekarar 1961 kuma shine Sarkir Fulani na goma sha biyar 15 da Gwamna Kano Ganduje ya nada shi a ranar 9 ga watan Mayu a shekarar 2020.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button