Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Daga yanzu na daina rungumar mata da sumbatar su a cikin fim da kuma rawa da waka, cewar jarumi Ali nuhu

Advertising

Jarumi Ali nuhu ficaccan jarumi ne a masana’antar kannywood wanda wasu suke masa lakabi da sarkin kannywood, sannan kuma ya kasance Darakta mai shirya fina-finai masu dogon zango.

Sai dai duk wanda yasan harkar fina-finan wasan kwaikwayo to tana dauke da wasu abubuwa wanda mutum zai iya sa kan sa a cikin kunya da bakin jini wajan aikata abubuwan da basu dace ba, duba da yadda harkar fim ta gaji domin a yanzu sun dauki harkar fim a matsyin wayewa wanda idan baka nuna wasu halaye a cikin harkar ba to baka waye ba.

A cikin abubuwan da ‘yan wasan kwaikwayon suke aikatawa wanda duk yawan shekarun ka kama daga Namiji ko Mace to tabbas girman ka na iya faduwa wanda kowa zai ga kamar baka rike mutuncinka ba.

Advertising

Cikin wadannan abubuwan suke kamar haka, Rawa a bainar jama’a a gidan gala, yawan hulta da ‘yan matan kowa yasan bana gari bane, wannan kadan daga ciki kenan.

Jarumi Ali nuhu wanda yake taka rawar gani a fina-finan masana’antar kannywood sannan kuma ya zamto babba a ciki wanda a yanzu haka ba’a kowane fim yake fitowa ba duba da yadda ya fara manyanta, inda jarumi Ali nuhu ya bayyana cewa daga yanzu ya dai na rawa da rungumar mata a cikin fim.

kamar yadda kuka sani a kwanakin baya wata bidiyon jarumi Ali nuhu ta bayyana inda a cikin bidiyon akaga yana sunbatar wata mata tare da rungumar ta al’amarin daya janyo cece-kuce a masana’antar kannywood, inda wasu daga cikin mabiyan sa a shafin sa na sada zumunta sukayi bakin ciki da wannan bullar bidiyon nasa.

Domin kuji cikekken labari kan wannan al’amarin sai ku kalli bidiyon dake kasa.

https://youtu.be/3lhWWWb7loA

Advertising

10 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button