Advertising
Advertising
Labarai

Kotu ta umarci bangaren Gwamna Abdullahi Ganduje da biyan tarar naira Miliyan daya 1M akan shigar da karar da yayi marar tushe

Kotu ta umarci bangaren Gwamna Abdullahi Ganduje da biyan tarar naira Miliyan daya 1M akan shigar da karar da yayi marar tushe

Wata babbar kotu dake Babban Birnin tarayya Abuja karkashin jagorancin mai shar’i Hamza Muazu ta tabbatar da cewa, a bangaren sanata Ibrahim Shekarau na Jam’iyyar APC ya yi shirin Zabe na shugabannin Jam’iyya a matakin karamar hukuma na mazabu a Jihar.

Advertising

A ranar talatin ga watan Nuwamba Alkalin Kotun ya amince da duk wani korafe-korafe na bangaren Ibrahim Shekarau da ya yi na cewa, bangaren Abdullahi Umar Ganduje bai yi zabeb shugaban Jam’iyya na mazaba ba.

Daga bisa kuma sai bangaren Abdullahi Umar Ganduje ya garzaya Kotun ya shigar da kara da kuma neman Kotun ta dakatar da sauraron karar, sannan kuma ya aka janye matakin da ta dauka na zaben shugabannin Jam’iyya na mazabar.

Advertising

Da yake yanke hukuncin karar ta bangaren Abdullahi Umar Ganduje, sai shar’a ya kori karar tasu sannan kuma ya cahe su tarar naira Miliyan Daya 1M, sakamakon karar bashi da tushe da kuma bata lokacin bangaren nasu Ibrahim Shekarau.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button