Advertising
Advertising
Labarai

Wani Malamin Makaranta dan kadar India ya ginawa Matar sa katafaren Gida na Naira Miliyan 140M

Wani magidanci dan kasar India ya ginawa Matar sa katafaren Gida mai kama da ficaccan Gida Taj Mahal.

Advertising

Mutumin wanda ya kasance Malamin Makaramta mai sunaAnand Prakash Chouksey ya bayyana cewa, an shafe shekaru uku 3 ana gina wannan Gidan na Madhya Pradesh wanda ya gina shi a matsayin kyauta ga Matar sa mai suna Manjusha mai shekaru 48 a Duniya.

Mutumin mai suna Chouksey mai wanda yake da shekaru 52 a Duniya ya sake bayyana cewa’ wannan katafaren Gidan da ya gina kyauta ne ga Matar sa.

Inda yake bayyana cewa: Ginin wannan Gidan yaci Dalar Amurka kimanin 260 wanda ya kai kimanin naira Miliyan 140M, inda aka gina wannan Gidan bisa taswirar Gidan Taj Mahal, wanda aka yi a Karni na 17 a birnin Agra da ke kusa da Kogin Yamuna a kasar Indiya, wanda yanzu ya zama abin al’ajabi a Duniya.

Advertising

Chouksey ya kara da cewa, da farko yana son kwaiwayon ginin Taj Mahal ya kai tsawon kafa 80, amma ya yi watsi da umarnin hukumomin yankin tare da rage shirinsa na ganin gidan zuwa kafa 29.

Sannan yace, daga wajen gidan ya dogara ne a kan nau’in ginin Taj Mahal, amma cikin gidan yana da karin tsari na zamani.

Yayin da masu fasaha daga West Bengal da Indore suka taimaka da fafe cikin gidan, masu sana’ar kira daga birnin Mumbai ne suka kera kujeru da sauran kayan daki na gidan.

Sarkin Mughal Shah Jahan ne ya gina ainihin gidan Taj Mahal don gina kabarin matarsa Mumtaz Mahal a 1632 Miladiyya.

Ga hotunan katafaren Gidan nan a kasa domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button