Wata fitsararriyar yarinya mai suna Farakhiyya tayi mummunan kalamai akan auren Sarkin Dau
Wata fitsararriyar yarinya mai suna Farakhiyya tayi mummunan kalamai akan auren Sarkin Dau
Farakhiyya ta bayyana cewa: Irin auren yarinya ‘Yar shekara sha bakwai 17 da Sarkin Daura hakan ya yi, to amma ya kamata suyi yaki akan wannan abu da yayi wanda bai dace ba.
A tunanin da Farakhiyya tayi tana tunanin irin wannan auren wurin da ake shi ne yake janyo kashe-kashe da kuma rashin zaman lafiya ta’addancin dake faruwa a Arewacin Nageriya, Farakhiyya tayi wannan wallafar ne a shafin ta na sada zumunta Twitter.
Inda tayi wallafar cikin harshen turanci kamar haka.
Alhamdulillah dan babban shehin malami ashe prof Muhammad sani umar R/lemo yayi mata martani mai hikima cikin ilimi da nunawa duniya ko wacece ita a al’ummarmu ga abinda yake cewa.
A yayin da duk duniyar mutane masu hankali kowa ya san cewa, irin matsalolin da muke fama da su ba komai bane suka haddasa su ba face zalunci da jahalici da rashin ayyukan yi da yawaitar rashawa da kuma rashin kyakkyawan shugabanci magance wadannan shi zai kawo mana sauki.
Ita kuwa “Sherlock Holmes” din arewa garkuwar tsaron duniya wayayyiya (enlightened) ‘Yar wayayyu ra’ayinta shi ne duk wannan halin da muke ciki shine auren wuri da ‘Yan arewa suke yi !! Da zarar kuma sun daina aikata hakan to nan duk wannan masifar zata kau watakilama mu zama tamkar Switzerland.
Irin wannan tunanin shine tunanin duk ‘Yan boko akidar da suke cikin musulmai suke dauke da shi yayin da masu hankali suka yi ittafaki akan abubuwan da suke kawo mana koma baya, da kuma abubuwan da yakamata a yi don warwaresu sukuwa gani suke auren wuri da littafan ibnu Taimiyyah da Bukhari da sauran littafan malaman musulunci sune musabbabin komai ba za a samu zaman lafiya ba sai an watsar da su.