Advertising
Advertising
Labarai

Wata Matashiya mai suna Shatu Garko ta lashe gasar Sarauniyar Kyau ta sami kyautar Mota da Miliyan 10M

Wata Matashiya mai suna Shatu Garko ta lashe gasar Sarauniyar Kyau ta sami kyautar Mota da Miliyan 10M

Wata matashiya dake zaune a Jihar Kano dake Arewa maso yammacin Nageriya mai suna “Shatu Garko” ta lashe gadar ta Kasa wanda aka gudanar a karo na 44 a Jihar Lagos a ranar Juma’a.

Advertising

Matashiyar Shatu Garko a yanzu haka ita ce sarauniyar kya wanda ta kada ‘Yam mata goma sha takwas 18 wanda suka zagayen gasar tare, kamar yadda Jaridar Guardian ta ruwai to wanda a yanzu haka ta gaji Etanyi Tukura dake Jihar Taraba.

Shatu Garko wanda a yanzu ita ce sarauniyar kyau ta bayyana din dadin ta akan cikar burinta da ta samu sannan kuma ta cimma babbar nasara, bayan haka ta mima godiyar ta ga wadan da suka hada gasar tare da Mahaifiyar ta wanda ta goya mata baya tare da bata kwarin gwaiwa.

Sannan kuma sarauniyar kyau Shatu Garko ta bayyana cewa: Bani da wani buri da ya wuce ganin na zama sarauniyar kyau ta Najeriya, ina matukar godiya ga wadanda su ka shirya wannan gasa, ina godiya ga mahaifiyata bisa goyon baya da kuma karfafa min gwiwa.

Advertising

Bayan Haka kuma an baiwa sarauniya Shatu Garko kyautar Naira Miliyan goma 10M da gida da motar hawa da kuma mukamin jakadiyar kyau ta Najeriya.

A ‘Yan shekarun baya dai jihohin Arewa maso yammacin Najeriya sukan kauracewa shiga gasar sabida tsaraicin da ake nunawa a bikin na sarauniyar kyau.

Sannan kuma jerin ‘Yan matan da su ka shiga gasar Sarauniyar Kyau, An soma gasar sarauniyar kyau a Najeriya tun a cikin 1957 da nufin karfafawa mata, kuma duk shekara ne ake gudanar da gasar tsakanin jihohin kasar nan.

Alkalai ne suke tantance ‘Yan takarar daga jihohin Kasar nan kafin zaben sarauniyar kyau, Haka kuma duk wadda ta lashe sarauniyar kyau a Najeriya ita ce ke wakiltar kasar a sarauniyar kyau ta duniya.

Ga hotuann a kasa domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button