Labarai

Yanzu-Yanzu: Sojojin Nageriya sun isa sansanin gawurcaccan dan ta’adda Bello Turji domin gamawa da shi

Yanzu-Yanzu: Sojojin Nageriya sun isa sansanin gawurcaccan dan ta'adda Bello Turji domin gamawa da shi

Daga Datti Assalafiyfi.

Wasu labarai da suke fitowa daga wata majiyar sirri na sojoji tace mayakan sojojin kundunbala sun isa babban sansanin Shugaban ‘yan ta’adda Bello Turji a jejin Gundumi dake karamar hukumar Isa jihar Sokoto.

Sojojin sun shiga jejin ne ta sama da kasa wato da tallafin jiragen yaki, kuma adadi mai yawa na mayakan Turji sun bakwanci lahira ba shiri, ana tunanin harin ya rutsa da Turji, a dayan bangare ana tunanin ya tsere saboda har zuwa yanzu ba’a gano gawarsa ba.

Muna maraba da wannan babban yunkuri da Gwamnatin Maigirma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tayi na kokarin shafe Turji daga doron Duniya.

Insha Allah Alkunuti da Musulmai suke ba zai fadi a banza ba, Turji yana dab da shiga babin tarihi, jinjina gareku sojojin Nigeria.

Muna rokon Allah Ya taimaki sojoji akan ‘yan ta’adda.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button