Advertising
Advertising
Uncategory

YANZU-YANZU: Madugun Kwankwaso na shirin ficewa daga PDP zuwa NNPP.

Tsohon Sanata kano ta tsakiya, Rabi’u Musa Kwankwaso, na shirin sake ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar New Nigeria Peoples Party wato NNPP.

Advertising

Tuni dai Sanata Kwankwaso a ranar Talata ya gana da shugabannin jam’iyyar ta NNPP a wani yunkuri na kammala zuwansa jam’iyyar da ake sa ran zai yi amfani da shi wajen neman takarar shugabancin kasar.

Sakataren jam’iyyar NNPP na kasa mai barin gado, Ambasada Agbo Gilbert Major ne ya bayyana hakan a Abuja, a wajen taron kwamitin zartarwa ta kasa (NEC).

Yace taron na da nufin daukar muhimman shawarwari da zasu mayar da jam’iyyar gabanin babban zaben 2023.

Advertising

A cewar shugaban kwamitin, nan da ‘yan kwanaki gwamnan jihar Kano da ya yi sau biyu zai koma jam’iyyar tare da abokanan tafiyar sa.

Ya kuma yi watsi da ba Kwankwaso tikitin takarar shugaban kasa kai tsaye, inda ya ce za a bai wa sauran masu son tsayawa takara tikitin.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button