Advertising
Advertising
Labarai

Yadda wata Matar aure mai suna Maryar Abubakar take zina da Dan Bindiga sabida talauci

Yadda wata Matar aure mai suna Maryar Abubakar take zina da Dan Bindiga sabida talauci

A cikin shekara ta 2021 kadai, yan bindiga da ke ayyukan ta’addanci a sassa daban-daban na Arewacin Najeriya musamman a yankin Arewa maso Yamma, sun kashe gomman mutane, tare da lalata dukiyoyi na miliyoyin Naira.

Advertising

Sannan kuma ‘Yan Bindigar sun kuma yi awon gaba da yara ‘yan makaranta da yawa, tare da neman kudin fansa domin sako su.

Bayan haka ‘Yan Bindigar sun kuma mayar da yankin ya zama wuri mafi rashin tsaro a kasar abin baƙin ciki duk da haka wasu matan da ya kamata su fahimci irin barnar da ‘Yan Bindigar ke yi.

Musamman yadda ayyuka ƴan bindigar suka shafi mata da yara, haka wasu matan irin su Maryam suka rufe ido suka cigaba da yi wa ƙungiyoyin masu ɗauke da makaman aiki.

Advertising

Wani abin damuwa ma shi ne matar aure da ake tsammanin ta zama uwa ta gari, itace yanzu ta iya ƙulla yin soyayya da daya daga cikin yan bindiga dake dajin Kaduna, ta kuma wadata su da yan uwanta mata don jin dadi.

Idan ba a manta ba a safiyar yau ne wani rahoto da gidan Talabijin na Channels TV ya fitar, ya bayyana cewa kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya Frank Mba ya bayyana kama wata matar aure mai shekaru 39 mai suna Maryam Abubakar, wacce saurayinta dan bindiga ne duk da cewa tana da aure.

Rahoton yace, Maryam wadda mijinta yana raye kuma yana gida, tana saduwa da daya daga cikin ‘yan bindigar, tare da wasu matan sannan suna kai musu abinci, da kayayyakin more rayuwa da ‘yan mata don jin dadi.

Har ila yau, suna taimaka wa ’yan bindigar wajen gudanar da bincike, da kuma ba su bayanai kan wani abin da aka sa a gaba wanda yin haka hakika wannan wani zagon kasa ne ga yakin da gwamnati ke yi da rashin tsaro a kasar.

Mutane irin su Maryam Abubakar da ke aiki da ‘yan bindiga, ko dai a matsayin masu ba da labari, ko kuma masu kawo kayayyaki, suna zagon kasa a yakin da gwamnati ke yi da rashin tsaro a kasar.

Za a iya cewa, kayayyakin da mutane irin su Maryam suke kaiwa ƴan bindigar ne ya sa ’yan ta’addan masu dauke da makamai samun saukin rayuwa a cikin dajin.

Har ila yau, idan ba tare da bayanai da abubuwan da mutane irin su Maryam, da sauran masu ba da labari suka ba wa waɗannan ‘yan bindiga ba, ‘yan bindigar ba za su iya rayuwa ba na dogon lokaci a cikin daji.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button