Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Malam Lawal Gajere wanda ake cewa ya nemi afuwar Mawaki Tijjani Gandu kan saka shi yada labarin karyar cewa ya rasu

Malam Lawal Gajere wanda ake cewa ya nemi afuwar Mawaki Tijjani Gandu kan saka shi yada labarin karyar cewa ya rasu

Kamar yadda kuka sani a kwana baya an yada labarin cewa, Ficaccan dan wasan barkwanci na Masana’antar Kannywood Malam Lawan Gajere ya rasu, inda wallafar labarin ta fito daga wajan Mawaki Tijjani Gandu.

Advertising

Wanda sai daga bayan kuma aka tabbatar da cewa Malam Lawan Gajere bai rasu ba, inda hakan yasa Mawaki Tijjani Gandu yaji babu dadi sabida sanarwar da yayi wasu zasu iya fassara ta da wani abu.

To a yanzu kuma wani saban labari ya bulla kan wannan labarin rasuwar Malam Lawan Gajere wanda Mawaki Tijjani ya wallafa, inda ake cewa Malam Lawan Gajere ya yaudari Mawaki Tijjani Gandu.

Ga dai yadda labarin yake.

Advertising

Malam dai ya yaudari Mawaki Tijjani Gandu ne ta hanyar sakawa a sanar da shi cewa ya mutu, alhalin kuma ya na raye, wanda wannan dalilin ya sa shi kuma Mawakin ya shelantawa duniya akan Malam Lawal din ya rasu.

Daga bisani kuma ya gano karya kawai Lawal Gajeren ya sharara masa, wanda wannan ta sa Tijjani Gandun ya dauki mataki a kan Malam Lawal Gajere din.

Domin kuji cikakken labarin matakin da Mawaki Tijjani Gandunl ya dauka da kuma yafiyar da Malam Lawal Gajere ya nema Tijjanin ya yi masa ta hanyar kamun kafa da jarumi Mustapha Naburaska don a ba shi hakuri, sai ku kalli bidiyon dake kasa.

Ga bidiyon nan domin ku kalla kai tsaye.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button