Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Jaruma Nafisa Abdullahi ta cikin shirin Labarina ta sami daukakar data kere ko wace Jaruma a Kannywood a shekarar 2021

Jaruma Nafisa Abdullahi ta cikin shirin Labarina ta sami daukakar data kere ko wace Jaruma a Kannywood

Tauraruwar fina-finan Hausa Naflsa Abdullahi na cikin jerin taurarin da aka fi neman karin bayani a kansu a shafin matambayi-ba-ya-bata na Google Search a shekarar 2021 a Najeriya. Tauraruwar ta fim din Labarina ta shiga jerin ne
tare da taurarin fim na kudanoin Najeriya da ake kira Nollywood irin su, Destiny Etiko, Tonto Dikeh, Zubby Michael.

Advertising

Sai dai Google ya saka Nafisa a bangaren Nollywood maimakon Kannywood, wanda nan ne take oiki ya zuwa Iokacin hada wannan rahoton, ita ce a matsayi na shida a sashen taurarin fina—finai bayan Destiny Etiko da Zubby Michael da Pere da Tonto Dikeh da Iyabo Ojo da kuma Olu
Jacobs.

Haka kuma, Nafisa ce kadai daga taurarin Kannywood data shiga cikin taurari 10 na farko a Google Search.

Advertising

Sauran ‘yan Kannywood Rahama Sadau da Fati Washa da Maryam Yahaya da Hadiza Gabon ne ke biye mata a shahara, duk da cewa ba sa cikin goman farko.

Shafin Google kan fitar da kalmomi da sunaye da ababen girki da mutane wadanda miliyoyin masu amfani da shafin suka fi bincikawa duk shekara, sannan shafin kan yi wa sunayen rukuni, inda ake da rukunan mawaka da wakar kanta da wasanni da ‘yan fim da fina-finan kansu da tambayoyin da aka fi yi.

Nafisa na da mabiya miliyan biyu a Instagram da 176,600 a Twitter da kuma wasu miliyan biyu a Facebook.

A bangaren fina-finai ‘yan Najeriya sun fi neman bayanai kan Squid Game da Coming to America 2 da Sex Life da Black Widow da kuma Red Notice, daga cikin wadanda suka rasu a 2021 kuwa, shahararren malamin Kirista TB Joshua da mawaki Sound Sultan da kuma Sani Dangote kani ga Aliko Dangote na cikin wadanda aka fi dubawa.

Kamar yadda bayanai suka nuna, Nafisa ta fara shahara ne a shafin daga ranar 3 zuwa 9 ga watan Janairun 2021, Hakan ba zai rasa nasaba ba da kammala kashi na 2 na fim dinta mai dogon zango wato Labarina, inda aka haska zangon karshe a karshen watan Disamban 2020.

Masu neman bayanai kan tauraruwar sun karu zuwa kashi 93 a watan Satumba, wanda a daidai Iokacin ne ake tsaka da haska kashi na 3 na Labarina.

Bugu da kari masu bincika Nafisa Abdullahi sun karu zuwa kashi 100 cikin 100 daga 5 zuwa 11 na watan Disamba, wannan kuma idan ba ku manta ba, yana da nasaba da kayayyakin kawa data kaddamar mai suna NAFCOSMETICS.
Mazauna Abuja babban birnin Najeriya ne suka fi neman bayanai game da Nafisa, sai kuma jihohin Rivers da Legas da Kaduna.

Fim din wanda kamfanin Saira Movies na Aminu Saira ke shiryawa ya samu Nafisa a matsayin babbar jaruma wadda aka gina labarin a kanta, tun bayan fara haska Labarina babu wani fim da Nafisa ta fito a ciki wanda ya yi kusa da farin jinin da Labarina ke da shi.

Yayin da tauraruwarta ke tsaka da haskakawa, ta kaddamar da sabon kamfanin kayan kwalliyarta mai suna NAFCOSMETICS a watan Nuwamban 2021.

Sannan kuma an san tauraruwar da tafiye-tafiye zuwa kasashen Turai da Amurka, inda takan je domin ƙarin karatu ko kuma yawon buɗe-ido.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button