‘Yan Bindiga sun kashe Mutane 38 sannan kuma sun kone Motoci da kayan abinci a Jihar Kaduna
'Yan Bindiga sun kashe Mutane 38 sannan kuma sun kone Motoci da kayan abinci a Jihar Kaduna
Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa, ‘Yan Bindiga suna kashe Mutane talatin 30 a hare-haren da suka kai karaamr hukumar Giwa.
Da farko dai Jami’an Sojoji da ‘Yan Sanda sune suka fara da ba rohoton cewa, Mutane ashirin 20 sun rasa rayukan su a harin da ‘Yan ta’adda suka kai Giwa.
Sannan kuma kwamisjinan tsaro da harkokin gida na Jihar Kanduna, Samuel Aruwan, a wata sanarwa da ya bayyana ya fadi cewa, ‘Yan Bindiga sun kai hari a kauyukan kauran Fawa Marke da Riheya garin dake Giwa inda suka hallaka Mutane 20.
Bayan haka ya kara da cewa: Motoci manya da kanana gami da kayan abinci na amfanin gona suma an kone su.
Gwamnan Jihar Nasir El-Rufai ya yi bakin ciki da wannan harin da ‘Yan Bindiga suka kai, inda ya yiwa iyalan wanda abin ya shafa ta’aziyya, a cewar Aruwan.
Sai dai kuma rahotannin da su ke fitowa yanzu sun baiyana cewa adadin mutanen da su ka rasa rayukansu a harin ya kai talatin da takwas 38, Kamar yadda Aruwan ya tabbatarwa jaridar DAILY NIGERIAN a yau Lahadi.
Bayan rahoton cewa ‘Yan ta’adda sun hallaka mutane 20 a karamar hukumar Giwa, Jami’an tsaro sun tabbatarwa gwamnatin Kaduna cewa adadin mutanen da a ka kashe ya ƙaru zuwa 38, a cewar Aruwan.
Sannan kuma an gano sunayen 29 da ga ciki, in da 9 kuma ba a kai ga gano sunayen su ba.
Ga sunayen Mutanen da suka rasa rayukan su a yayin wannan harin da ‘Yan ta’adda suka kai.
1. Rabi`u Wada
2. Salisu Boka
3. Alh Nura Nuhu
4. Alh Bashari Sabiu
5 Alh Lawal Dahiru
6. Abbas Saidu
7 Inusa Kano
8 Malam Lawal Nagargari
9. Malam Aminu
10. Lawal Maigyad
11. Alh Mustapha
12 Lawal Aliyu
13 Sale Makeri
14 Sani Lawal
15 Auwal Umar
16 Jamilu Hassan
17 Badamasi Mukhtar
18 Malam Jibril
19 Lawal Tsawa
20 Sule Hamisu
21 Sadi Bala
22 Kabiru Gesha
23 Abubakar Sanusi
24 Saiph Alh Abdu
25 Haruna Musa
26 Lawal Hudu
27 Malam Shuaibu Habibu
28 Malam Yahaya Habibu
29 Abubakar Yusuf.