Advertising
Advertising
Labarai

Wata Budurwa ta kusan shekawa Lashira bayan ta sha guba sabida Saurayin ta ya juya mata baya

Wata matashiya mai shekaru ashirin da hudu 24 dake unguwar Sabuwar Gandu a birnin jihar Kano, ta yi yunkurin shan guba don ta kashe kanta sabida Saurayinta ya fasa aurenta, kamar shafin Hausaloaded suka ruwaito.

Advertising

An yi ranar ceto ran Budurwar mai suna Aisha Ibrahim bayan da aka yi kiran gaggawa ga rundunar ‘yan sandan jihar Kano.

Inda nan take aka aike da dakarunmu wurin inda aka ceto rayuwar Aisha bayan da aka kai ta asibitin kwararru na Murtala Mohammed dake Kano, sannan aka kwace shinkafar beran da ta yi yunkurin amfani da ita, a cewar kakakin ’yan sandan jihar “DSP Abdullahi Haruna Kiyawa”.

Aisha Ibrahim ta bayyana cewa, baza ta iya rayuwa babu wannan saurayin nata ba duk da ya juya mata baya, inda ya maida soyayyar sa ga wata Budurwar.

Advertising

Aisha take cewa, Na sayo shinkafar bera da nufin naci sabida ba zan iya jurar ganin yana rayuwarsa tare da wasu matan ba, gara na mutu na gaji da wannan duniyar.

Ina matukar kaunarsa wanda hakan ne ya sa na zabe shi a matsayin wanda zan aura amma ban san cewar yaudarata yake yi ba, maganar gaskiya ba zan yafe masa ba.

Wannan ne karo na biyu da Aisha take yunkurin kashe kan ta, Mahaifiyar Aisha wanda an sakaya sunanta ta bayyana cewa, wannan shi ne karo na biyu da ’yar tata ke yunkurin halaka kanta.

Inda Mahaifiyar tata tace, Akwai lokacin da ta taba yin irin haka ta sha sinadarin Hypo aka ba ta madara, wannan karon kuma ’yan sanda sun ceto ta bayan ta sha shinkafar bera, ban taba tsammanin zata sake aikata irin wannan abu ba wai da sunan soyayya.

kakakin ’yan sandan yace, an fara bincike don gano hakikanin abin da yasa take kokarin shekawa lahira.

Kakakin ya gargadi jama’ar gari da su kiyayi yunkurin kashe kansu yana mai cewar duk wanda aka kama za’a mika shi zuwa kotu don yanke masa hukunci.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button