Addu’ar muce take bin Maryam Yahaya shi yasa ta kwanta jinya kan wulakancin da tayiwa Dan uwan mu, Daga wata Budurwa
Wani sajtin murya na wata Budurwa da ya karade shafukan sada zumunta ya dauki hankulan kan yadda wata matashiyar Budurwa take bayyana cewa, addu’ar su ce take bibiyar Jaruma Maryam Yahaya shi yasa take cikin halin rashin lafiya.
Budurwar ta bayyana kan ta a matsayin kanwar matashin nan da a kwanakin baya ya yi tattaki daga Jihar Yobe har zuwa Jihar Kano domin ya sami ganin Jaruma Maryam Yahaya, amma ko da yaje Kano sai Jaruma Maryam Yahaya taki yarda su hadu.
Wanda hakan ya sa Matashin ya sha fiya-fiya yake yunkurin kashe kan sa amma duk da hakan Maryam Yahaya bata je ko asibitin ba domin taga halin da yake ciki.
Ta bayyana wannan abi ya daga hankalin dangin su da ‘Yan uwa kan wannan abu da Maryam Yahaya tayiwa Dan uwan su, wanda a dalilin hakan suke ta addu’ar Allah ya saka musu sannan tace addu’ar su ce Allah ya amsa shi yasa ya jarrabi Maryam Yahaya da rashin lafiya.
Ga dai cikekkiyar bidiyon a kasa domin ku kalla.