Duk Namijin da yake barin Matar sa tana bidiyon rawa a TikTok ko kamshin Aljanna bazai ji ba, cewar Jaruma Rukayya Dawayya
Duk Namijin da yake barin Matar sa tana bidiyon rawa a TikTok ko kamshin Aljanna bazai ji ba, cewar Jaruma Rukayya Dawayya
Ficacciyar Jarumar Masana’antar Kannywood Rukayya Dawayya tayi wani bayani akan Matan da suke bayyana a cikin bidiyon TikTok suna rawa da wata, inda Jarumar ta bada wani labari wanda take abin ya auku a kan ta lokacin tana da aure.
Inda Jarumar yake fadin cewa: Jarumar ta fara da bayyana yadda wasu shakikan kawayenta su ka kai mata ziyara gidanta da ke Abuja bayan ta ci kwalliya amma Mijinta bai gani ba.
Tun samun labarin sun kai mata ziyarar our ta nuna a sanar dasu cewa bata nan duk don kada su ga kwalliyar ta kafin Mijinta, a cewar jarumar har sai da Mijin ta ya dawo ya ga kwalliyar sannan daga bisani ta kira su ta ce musu ta dawo daga inda ta je.
Daga karshen bidiyon Jarumar ta bayyana cewa: Duk macen da take yin kwalliya ta wallafa bidiyon kwalliyar a dandalin TikTok bata son Mijin ta, yayin da mazan da su ke barin matan su suna bidiyon ba sa kaunar matan kuma basa kishin su.
Jarumar ta kara da cewa: Ko kamshin Aljannah namiji mara kishi ba zai ji ba sabida hakan fadin manzon Allah (SAW) ne, sannan tace da a ce mata zasu ga wasu mazan da suke kallon bidiyon su na TikTok da ba su yi ba tun farko da har kuka sai sun yi.
Jarumar ta kara da cewa: Duk macen da ta ke son mijinta tana killace kanta ne tare da boye surar jikinta, mijinta kadai zata bayyana wa su.
Daga karshe jarumar ta yi addu’a inda take fadin cewa: Allah ya yi mana maganin bala’in da ya shigo wai shi TikTok.