Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Gaskiya tayi halin ta akan maganar auren Adam Fasaha tsohon mijin Momee Gombe da Nana ta shirin Izzar so

Gaskiya tayi halin ta akan maganar auren Adam Fasaha tsohon mijin Momee Gombe da Nana ta shirin Izzar so

Kamar yadda kuka sani a kwanakin baya da suka wuce Adam fasaha tsohon mijin Jaruma Momee Gombe ya wallafa wasu hotuna tare da Jarumar shirin Izzar so wato Nana, inda kowa yake Jama’a suka yi ta tofa albarkacin bakin su.

Advertising

Duba da hotunan da suka dauka kowa yana tunanin aure zasu yi domin akan wallafa irin wadan nan hotunan kafin aure wanda a turance ake kiran sa da Pree Wedding Picture.

To a yanzu kuma mun sami wani labari dangabe da maganar auren nasu inda Adam fadaha yake nuna cewa, wannan hotunan da suka dauka da Nana Izzar so shiri ne da aure zasu yi ba har ma yake fadin cewa gobe zai fitar da wakar sa mai suna Ma’aurata.

Wanda hakan yana nuna tabbacin ba aure zasu yi ba sun dauki wadan nan hotunan ne domin shirya wasu abubuwan su, wanda har yake fada da bakin sa yake cewa shiri ne ba aure zadu yi ba.

Advertising

Ga dai wallafar rubutun da Adama Fasaha yayi akan sabuwar wakar sa da zai fitar da ita mai suna Ma’aurata.

Gobe litinin 20/12/2021 insha Allah zansaki sabuwar wakata audio mai suna MA AURATA wadda muka rera da naja ta annabi, Zaku iya samunta a YouTube channel dina Adam fasaha tv kuyi Mana subscribe domin samun sabbin ayyukanmu da zarar mundora.

Sannan kuma ga wasu sabbin hotunan da Adama Fasaha tare da Nana ta shirin Izzar so suka wallafa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button