Nafisat Abdullahi: Kwararan dalilan da suka saka na dena Film din Labarina.
Jarumar Kannywood Nafisat Abdullahi ta bayyana irin dalilan ta na dena fitowa a Film dinnan mai dogon zango labarina.
Nafisat Abdullahi ta kasance jaruma mai tashe a cikin shirin wanddda fitar ta a Film din zai saka mutane da dama su dena kallon shirin, sabida da yawan mutane suna kallon Film din saboda ita ne.
jarumar ta fadi haka ne a wata tataunawa da gidan Radio a garin kano sukai da ita a daren shekaran jiya. Amma sai dai a dalilin da jarumar ta bayar sun hada da cewar yanzu kasuwancin ta bazai barta ta ringa harkar Film ba. Haka kuma tace dama sun samu sabani da masu Film din.
Sai dai gidan Radio sun so suji wana irin sabanine amma jarumar bata fadaba, Hausadailynews.com tayi kokarin jin wane irin dalili ne yasa ta dena wakilin mu ya tambayi mashiryin Film din wane dalili ne yasa jarumar tace ta bari sai dai ya kasa cewa komai.