Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Habaice habaice na kokarin kunno kai a Kannywood bayan cire Rarara a kamfen din Tinubu.

Habaice habaice na kokarin kunno kai a Kannywood bayan cire Rarara a kamfen din Tinubu.

Advertising

Yanzu ta tabbata an cire sunan Mawakin Dauda kahutu rarara daga kamfen din dan takara shugaban kasa a jam’iyyar APC Ahmed Bola Tinubu.

Tun bayan da mawakin ya saki wata sabuwar wakar sa mai taken suna lema ta sha gwaya, Ce-ce ku-ce yake ta yawo a gari akan wani baiti da mawakin ya saki, “Ka ce a cire suna na wannan na ji, / Da ma ban ce a saka ni ba inda ka ji, / Duk wani taro da ka ke don ni to na ji, / Mu harkar Tinubu ba sai da takarda ba.”

https://www.instagram.com/tv/Cj5QYn8jWUW/?igshid=YmMyMTA2M2Y=

Tu bayan sakin wakar wasu daga cikin abokan harkar sa sukaji dadin abun, amma daga bisani da ce-ce ku-ce ya barke na tsire sunan mawakin daga kamfen din Tinubu aka maye gurbin sa da Abdul Amart shi kuma ya sunan sa a matsayin memba.

Advertising

A cikin ayarin sunayen na farko da aka fitar, wanda mujallar Fim ta ba da labarin, Rarara ne jami’in gudanarwa (admin officer), sai dai kuma a wannan karon da aka cire shi sai aka mayar da muƙamin sa zuwa kudu, aka ba wata mai suna Eberechukwu Chidera Eberechi daga Jihar Inugu.

Dayawa wasu daga cikin yan masana’antar kannywood sunyi murna da cire Rarara, Wasu kuma suna farin ciki kasancewa an maye gurbin Rarar da da Abdul Amart maikwashewa.

An Dade ana takun saka a Kannywood tsakanin Rarara da Abdul Amart Tun bayan kafa kungiyar YBN Network da kuma kungiyar 13×13 movement da Rarara suka kafa.

Sai dai wata majiya ta bayyana mana cewa
an cire Rarara ne saboda a yanzu ba ya goyon bayan jam’iyyar APC a Jihar Kano sai Jam’iyar ADP.

Tun bayan bayyanar sabon jerin sunayen, Rarara bai ce uffan ba. Hasali ma ya na Gombe tare da jama’ar sa na kungiyar 13×13 Movement su na daukar sababbin wakokin sa irin su wakar ‘Jagaba Shi Ne Gaba’, ‘Lema Ta Sha Ƙwaya’, wakar gwamnan Gombe, da wasu wakokin hadaka da su shi da sauran mutanen sa, ya bar masu surutu su na yi.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button