Shahararran marubucin nan Datti Dattifi ya wallafa wani dogon bayani akan kaunar da yakewa Shugaba Mubammad Buhari
Shahararran marubucin nan Datti Dattifi ya wallafa wani dogon bayani akan kaunar da yakewa Shugaba Mubammad Buhari
GASKIYA NE MUNA KAUNAR SHUGABA
BUHARI. Daga Datti Dattifi.
Ba shakka nima ina cikin tsananin damuwa a duk kokacin da na wayi gari naga masoyan shugaba Muhammadu Buhari Maigaskiya suna raguwa, tsakani da Allah bana jin dadin haka saboda soyayyar da nake yiwa shugaba
Buhari don Allah.
Da yawan matasa da muka fara gwagwarmayar kare martaban shugaba Buhari a wannan kafar sun dawo daga
rakiyarsa, wasu saboda bukatarsu na neman kudi bata biya ba, wasu kuma saboda suna ganin Buhari ya gaza, yau sun dawo suna yakarsa.
Babu dadi a abinda yake faruwa da shugaba Buhari mutanen banza ‘yan iska maciya amana matsafa sun dabaibaye shi, sun rabashi da masoyansa na gaskiya, sun
nesanta tsakaninsa da talakawansa, yau Buhari ya dawo abin zagi da abin kyama a tsakanin talakawan Arewa.
Akwai wadanda suke ganin hatta Datti Assalafiy da ya gagara rabuwa da shugaba Buhari saboda ana biyan Datti Assalafiy ne, masu wannan zargin su ji tsoron Allah su
dena babu wani wakilin Gwamnatin Buhari.
Da yake bani kobo akan in kare muradin Buhari a social media, inayi saboda Allah ne da kuma abinda na fahimta game da gaskiyar Buhafi.
Bai dace ace gaba dayan mu mun rabu da shugaba Buhari ha a daidai lokacin da yake bukatar addu’ah da support daga garemu ba, zagi da tsinuwa da ake masa baya amfanar da komai, domin inda zagi da tsinuwa yana shiryar da mutum ya gyara wani kuskure da yakeyi.
To da munga haka a tare da Buhari Misali idan muna ganin Buhari ya |a|ace to duk inda ya kai tsanani ga |a|acewa har yanzu dai yana nan a matsayinsa na ‘dan uwa Musulmi, balle kuma Buhari bai |a|ace ba.
Sai dai ya gaza a himmarsa na gyara matsalar tsaron Arewa, magana na adalci Buhari yayi kokari a wasu bangarori, amma ba shakka ya gaza a fannin tsaro da kuma price contro.
Ya kamata ace kullun muna daukar darasi muna tuna baya akan abubuwa da suke faruwa, matsalar tsaron Arewa ajandace babba wanda tafi karfin shugaba Buhari da duk wanda muke zato zai iya magancewa, kuma ba akan komai ake yakar Arewa ba.
Sai don mun kasance Musulmai da kuma saboda arzikin karkashin kasa da Allah Ya mana
Buhari ba zai iya kalubalantar ajandar turawa da kafurai ba akan Arewa, wannan abin yafi karfin sa.
Sai dai ya lallaba ya karasa sauran wa’adin watanni da ya rage masa, yayi resignation shima ba alheri bane garemu, domin matsalar ta wuce duk yadda muke tunani Ina jiye mana tsoro kar sai Buhari ya gama mulki mu dawo yabonsa kamar yadda a yanzu wasu suke yabon Goodluck Jonathan.
Domin kullun gaba akeyi ba baya ba, abubuwa gara dagulewa suke da tabarbarewa, tsarin mulkin Demokaradiyyah yaudara ne, bai taba zama mafita ga matsalolin mu.
Idan muka duba manyan Arewa da kyau bamu da wani jan gwarzo da zamuyi alfahari dashi a matsayin jagora da zai iya magance mana matsalarmu, duk wanda aka kawo idan
an duba sai aga yana da tabo Buharin dai muka kyautatawa zato shima yau ya dawo abin tuhuma, ribar da talakan Arewa zai samu shine ya gyara tsakaninsa da Allah domin kar ayi biyu babu.
Muna rokon Allah Ya kawo mana sauki a Arewa, Allah Ya amintar damu daga dukkan sharri ba don halin mu ba.
Mun dauko wannan wallafar labarin ne daga shafin Rariya Hausa dake kan dandalin Facebook.