Advertising
Advertising
Labarai

Wasu Tagwaye Maza ‘Yan biyu wanda sun kasan ce Mawakan Hausa zasu angwance da ‘Yan Matan su wanda suma Tagwaye ne

Wasu Tagwaye Maza 'Yan biyu wanda sun kasan ce Mawakan Hausa zasu angwance da 'Yan Matan su wanda suma Tagwaye ne

Kamar yadda kuka sani a wannan lokacin an fitar da wani sabon salo na auratayya tsakanin tagwaye Maza da Mata, ma’ana shi ne tagwaye Maza wanda ake haifar su tare sukan hada kan su domin neman Mata tagwaye irin su wanda suma tare aka haife su, domin ku kulla auratayya a tsakanin su.

Advertising

T a yau ma mun sami wata wallafa daga shafin Rariya Hausa dake kan dandalin Facebook, inda suka wallafa wani hotunan tagwaye Maza da Mata da suka shirin kulla auratayya a tsakanin su.

Wadan nan tagwayen Maza wanda zasu auri tagwaue Maza sun kasan ce Mawaka Hausa, wanda a yanzu suke shirin angwancewa da wasu Mata wanda suna tagwaye ne kamar su.

Advertising

Kamar yadda shafin Rariya Hausa suka wallafa wani dan gajeren rubutu akan auren nasu kamar haka.

Za a daura auren mawakan Hausa Tagwayen Asali (Hassan Sani Abubakar da Hussaini Sani Abubakar) da Hassana Abdu Bawa da kuma Hussaina Abdu Bawa a Dutsin-Ma jihar Katsina ranar Asabar 8 ga watan Janairun 2022.

Allah Ya sanya alheri

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button