Labarai
Al’ummar Gabashin Yauri dake Jihar Kebbi suna zaman dar-dar tare da shirin tserewa sabida matsalar tsaro
Al'ummar Gabashin Yauri dake Jihar Kebbi suna zaman dar-dar tare da shirin tserewa sabida matsalar tsaro
Matsalar tsaro: Mutanen Gabashin Yauri dake Jihar Kebbi suna zaman dar-dar. Daga Ahmed Sarkin Yaki Yauri.
Mutane na cigaba da tserewa a Garuruwan su don tsira da rayuwan su, a wasu yankuna na Jihar Kebbi da suka hada da, Tungan Bindiga, Tungani, Mai kaho, Kimo, makaman tansu.
Hakan na zuwa ne bayan samun labarin dake cewa wasu masu dauke da makamai sun kai hari a wani yanki na Garin Kimo.
Wasu mazauna yanki na suyi kira da a sama musu da zaman lafiya k0 zasu cire amfanin gonakin su, Mutane dai na tserewa da mata da kananan yara izuwa cikin garin Yauri don neman mafaka.
Kawo yanzu dai babu wani cikaken bayanin ko sunyi barna ko aka sin haka.