Advertising
Advertising
Labarai

Shugaban Kasa Buhari ya bada umarnin raba Tan 40,000 ta Hatsi ga mabukata domin bukukuwan Easter da Sallah

Shugaban Kasa Buhari ya bada umarnin raba Tan 40,000 ta Hatsi ga mabukata domin bukukuwan Easter da Sallah

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da’a gaggauta fitar da tan 40,000 na hatsi iri daban-daban daga rumbun gwamnati domin taimakawa marasa galihu a Nijeriya wajen gudanar da bukukuwan Easter da Sallah masu zuwa.

Advertising

Ministan Noma da Raya Karkara, Muhammed
Mahmood ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar gwamnati bayan ganawar sirri da Buhari a fadar Shugaban kasa dake Abuja a ranar Talata.

Mahmood yace, Shugaban kasar ne ya gayyace shi tare da umartar sa da ya raba kayayyakin ga mabukata, inda ya kuma bayyana fatansa na cewa hakan zai rage radadin hauhawar farashin hatsi a kasuwa.

A cewarsa, ton 12,000 daga cikin tan 40,000 da aka amince da su, za’a baiwa ma’aikatar kula da jin kai da bala’o’i da cigaban jama’a ta tarayya domin rabawa ‘yan gudun hijira a fadin kasar nan.

Advertising

Na 20 nan da yammacin ranar ne sakamakon
sammacin da Shugaban kasa ya yi masa.

Ya ba da umarnin kuma ya amince da fitar da hatsi daga Ma’aikatar aikin Gona da Raya Karkara ta Tarayya, in ji Mista Mahmood yana cewa.

Don a sanya hatsi a araha ga mutane don yin bukukuwan Ramadan, Ista da Sallah.

Zamu kuma bada wasu hatsi ga ma’aikatar
jin kai don yin rabon.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button