Labaran Kannywood
Hoton amarya da angon jarumar izzar so da Furodusa mai shadda sun gigiza kannywood.
Wani hoton jaruma Shirin izzar so Aisha Najamu da Furodusa Bashir mai shadda sun tada hankula masoyansu, wanda haka ya ke nuna cewa kaman aure zasu.
Advertising
Tuni masoyan nasu suka fara yi musu fatan Alkhari wandda mutane da dama ke zata jaruman angwance zasi. Sai dai daga baya an gane cewar hotunan tallan kaya ne suka dauka.
Wannan ba shine karo na farko da jaruman kannywood ke saka mutane a rudani ba, Ko a kwanan baya wasu hotunan jarumi Yakubu Muhammad da fitacciyar jaruma Fati wahsa suka karade kafar sada zumunta wanda mutane da dama sukai zatan aure zasi.
Irin haka ma ta faru da jarumi Ali Nuhu wanda sukai tallan gidan biki shida wata budirwa.
Advertising
Advertising