Young Uztaz yayi jan hankali tare da fadakarwa kan Mutanen da suke surutai game da juna biyun Matar Buhari
Young Uztaz yayi jan hankali tare da fadakarwa kan Mutanen da suke surutai game da juna biyun Matar Buhari
Kamar yadda kuka sani Matar shugaban kasa Muhammad Buhari ta sami juna biyu wanda Jama’a suke ta maganganu a kai har ma abin yake neman wuce gona da iri.
Inda ake ta yada hotunan Matar tasa tare da fadin maganganu daban-daban wanda hakan bai dace ba, mai makon a tsaya iya maganar rashin tsaron dake damun Nageriya amma sai aka sauya layi ake abin da bai zama dole ba.
To a yau mun sami wata bidiyo daga Tashar Kundin shahara dake kan manhajar Youtube inda Ficaccan Malamin nan maj yawan fadakarwa fa al’umma, yake jan hankali ga Mutanen da suke maganganu akan juna biyun da Matar shugaba Buhari ta samu.
A cikin bidiyon da zaku kalla a kasa zakuji yadda Young Ustaz yake jan hankalin Mutane akan abin da suke fada game da juna biyun da Matar shugaba Buhari ta samu.
Sannan kuma yana mai kara fadin cewa ya kamata al’umma su karkato hankalin su kan abbubuwan da duke faruwa a wannan lokaci, na rashin tsaro da kuma ta’addancin dake faruwa a Arewacin Nageriya.
Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.