Advertising
Advertising
Labarai

Datti Assalafy yayi martani ga Mutanen da zasu fita yiwa shugabanni zanga-zanga a Arewacin Nageriya

SAKO GAREKU MASU SHIRIN FITA ZANGA-ZANGA A AREWACIN NIGERIA. Daga Datti Datti Assalafyfi.

Advertising

Tun jiya ake shiri a wasu Jihohin Arewacin Nigeria cewa yau za’a fara fitowa zanga-zanga domin bayyana bakin ciki da damuwa akan matsalolin tsaro da ya addabi Arewa ba tare da Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta dauki matakin da ya dace ba.

Ni Datti Assalafiy sakona gareku masu shirin fara fita zanga-zanga, ku sani cewa dokar kasa ta baku wannan damar matukar zanga-zangar lumana ne.

Amma ina baku shawara kar a bar wani ya dauki makami, kar a kyale kowa ya taba kayan wani k0 kayan Gwamnati, Mu sani cewa Nigeria tana kan tsini ana neman duk wata hanya da za’a haddasa mummunan yaki a Nigeria, amma hakan ba zai faru ba sai idan ‘Yan Arewa sun bada hadin kai.

Advertising

Wadannan miyagun ‘Yan siyasa makaryata mayaudara da muke gani sun tara kudin haram sun saita hanya a shirye suke da zaran wutar yaki ta kunnu a Nageriya su
kwashe matan su da ‘Yayan su da karuwansu su tsere daga Kasar a barmu cikin wahala muna konar kasarmu.

A karon farko na goyi bayan a fita zanga-zanga domin a ladabtar da Gwamnatin Muhammad Buhari, amma a kula sosai banda ketare iyaka mu aza kishin kasarmu da yankin mu a gaba.

Allah Ya taimakemu.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button