Labarai
Maharan ‘yan Boko Haram sun harba roka a yayin da shugaba Buhari zai kai ziyara maiduguri

Kamar yadda wasu suka sani daga cikin ku shugaban kasa Muhammad Buhari yayi niyyar kai wa ziyara garin maiduguri, amna sai aka yi rashin sa’a ‘Yan Boko Haram suka har ba roka a filin jirgin sama na Ngomari a yau.
Kamar yadda Jaridar Daily Nigeria ta ruwaito cewa, roka guda daya da aka harba ta sauka ne a Ajilari kusa da filin saukar jirgin sama inda sansanin sojoji yake.
Amma wata majoyar ta bayyana cewa, Mutum daya ya rasa ran sa a Ngomari, bayan kaha kuma wasu Mutanen sun sami raunika a Ajilari.
Ga hotunan inda roka ra sauka nan domin ku kalla.