Labaran Kannywood
wani saban video jarumar kannywood Momee Gombe ya tashi kan jama’a.
Shaharariyar jarumar kannywood maimunat Abubakar Wanda akafi sani da Momee Gombe ta Fitar dawani sabon video ta Wanda ya janyo Mata cece kuce awajan jama’a.
Momee Gombe tana daya daga cikin jaruman kannywood Mata Wanda a wannan lokacin tauraran ta ke haskawa sakamakon irin kokarin da take yi wajen aikinta.
Fitacciyar jarumar tafara samun daukaka ne tun lokacin data rabu da tsohon mijinta mawaki Adam fasaha inda dawowarta tafito acikin wasu wakokin Hamisu Breaker da jarumi Adam A zango kana daga bisani ta fata fitowa cikin fina finai.