An bayyana wasu daga cikin Jaruman Kannywood da suka daukaka a wannan shekarar ta 2021
An bayyana wasu daga cikin Jaruman Kannywood da suka daukaka a wannan shekarar ta 2021
Kamar yadda kuka sani a wannan shekarar da muke ciki ta 2021 Jaruman Masana’antar Kannywood da dama sun taka rawar gani, wanda a yanzu aka kawo wasu daga cikin wanda suma sum taka leda a Masana’antar a wannan shekarar ta 2021.
Lawan Ahmad wanda shima Ficaccan Jarumi ne a Masana’antar shirya Fina-Finan Hausa ta Kannywood wanda ya jima a Masana’antar ana damawa da shi.
Jarumi Lawan Ahmad ya taso a cikin shekarar 2021 a cikin wani film din sa mai suna izzar so wanda film din ya daga tauraruwar Jarumin sosai, bisa irin fadakarwar da ake yi a cikin film din hakan ya sa ake cewa Jarumi Lawan Ahmad mai gaskiya.
Sai Ummi Rahab wanda ita ma Jaruma ce a Masana’antar shirya Fina-Finan Hausa ta Kannywood wanda tun tana karama aka fara nuna mata yadda harkar Fim take, bayan data girma a yanzu sai aka fara sanya ta a cikin shiri mai dogon zango Farin wata sha kallo wanda Jarumi Adam a zango ya shirya shi.
Bayan nan kuma sai ta koma fitowa a cikin film mai suna Wuff wanda Lilin Baba yake shiryawa, bayan rikicin da sukayi da uban gidanta Adam A Zango wanda har yau basa jituwa a tsakaninsu.
Daddy Shikima wanda a yanzu kowa yafi sanin sa da Abale wanda yake yawan bayyana a shirin Fina-Finai masu dogon zango irin su Labarina, Aduniya, Sanda, da dai sauram su.
Adam Abdullahi Wato Daddy Hikima sanda ya shigo Kannywood yazo a mai bada kayan da jarumai suke sakawa wanda daga baya saiya fara fitowa a fina finai wanda yake fitowa a bangaren dan daba hakan yasa yayi fice a cikin fina finai irinsu Aduniya, Sanda, Haram Da Farin wata Sha Kallo, sunashi ya zageye kannywood akance mishi Abale Ko Ojo.
Sai kuma sabuwar Jarumar nan ta cikin shirin nan mai dogon zango wato Izzar so wanda a yamzu tauraruwar ta take kan haskakawa wato Ausha Najamu wanda a cikin shirin ake mata lakabi da Hajiya Nafisa.
Aisha Najamu sabuwar jaruma ce wadda film din daya nunawa duniya wace ita shine Izzar so wanda film din shiyasa ta sami masoya sosai a fadin duniya musamman irin fitowar da takeyi a cikin fim din ta rashin mutunci, jarumar yanzu tana daga cikin kyawawan jaruman kannywood masu tarin masoya wanda itama ta shiga dandalin tiktok yana gabatar da bidiyo kala kala.
Nuhu Abdullahi Shima tsohon jarumi ne wanda ya dade yana fitowa a cikin fina finan hausa amman ya sami Karin daukaka a cikin sabon film maoi dogon zango mai suna LABARINA wanda ya fito a matsayin Mahmud, kuma shine tsohon saurayin Fati Washa wanda yaso ya aureta yayinda ake hira dashi yake cewa zai iya aurenta, amman kuma kawai akaji batun aurenshi da wata.
Nafisa Abdullahi Kamar yadda kowa ya sani Nafisa tsohuwar jaruma ce wadda ta dade sosai a kannywood tayi manya manya fina finai har aka dena yayin jarumar a kannywood sai bayan fitowar shirin LABARINA jarumar ta dawo tashe sosai a kannywood, saide yanzu haka jaruma Nafisa Abdullahi tana kokarin fita daga cikin shirin ko kuma muce tana fice wadda aka samu Fati washa ta maye gurbinta a cikin shirin.
Rabi’u Rikadawa ko kuma muce Baba Dan Audu ya kasance tsohon dan wasan kannywood wanda ya taka rawa sosai a masana’antar kannywood shima ya kara samun daukaka ne a fitowar da yayi a cikin shirin Labarina wanda ya fito a wata fitowa mai burgewa, ya fito a bayan kudi a cikin shirin wanda ake tunanin cewa shi mahaifin Mahmud ne a cikin shirin.