Jami’an tsaro sun kama Mutumin da yake sayan Bindugogi a wajan ‘yan ta’addan da suka tuba
Jami'an tsaro sun kama Mutumin da yake sayan Bindugogi a wajan 'yan ta'addan da suka tuba
An gano yadda tubabbun ‘yan ta’adda suke boye Bindugogi daga baya kuma sai su sayar wa wasu ‘yan Bindugar.
Kamar yadda muka sami wannan labarin daga shafin Hausaloaded kamar yadda shima ya wallafa wata bidiyo da ake bincikar daya daga cikin ‘yan ta’addan da suke aikata wannan laifin.
Ga kadan daga cikin labarin.
Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya ta yi nasarar kama wani mutum da ya ke sayar da bin digogi ga ƴan ta’adda.
Kakakin rundunar SP Gambo Isah ne ya sanar da Nasarar ga manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Katsina a ranar Alhamis.
Dan ta’addan mai suna Sani Mamuda wanda ake ma laƙabi da Shaɗari yana zaune ne a ƙauyen Shama da ke ƙaramar hukumar birnin Magaji a jahar Zamfara.
Jami’an ƴan sandan sun kama shi a kan hanyar ƙananan hukumomin Kurfi zuwa Batsari na jahar Ƙatsina, inda aka same shi da bindigigo ƙirar AK-47 ɓoye a cikin sit ɗin babur tare da harsashi guda 42.
Ga cikekkiyar bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.