Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Daraktan shirin Labarina Aminu Saira ya fara shan suka game da shirin Fim din Labarina

Kamar yadda kuka sani a halun yanzu al’umma masu kallin shirin Labarina mai dogon zango sun fara kosawa da kallon shirin, duba da yadda al’muran Fim din suka fara tabarbarewa.

Advertising

Labarina shirin wanda a farko ya ja hankalin al’umma wanda take ta yabon sa tare da nuna goyon baya wajan kallon shirin a duk sanda za’a harka shi.

Sai dai kuma bayan shirin ya sami karbuwa a wajan al’umma sai a aka fara wasu abunuwan da al’umma zasu yi baya-baya da kallon shirin, inda aka bayyana Mahmud ya rasu a cikin shirin, sannan kuma aka nuna anyi garkywa da Sumayya.

Wadannan Jaruman shirin guda biyu za’a iya cewa sune manyan taurarin da suke harkakawa a cikin shirin wanda tun farko sune suka fi taka rawar gani.

Advertising

Bayan haka an shafe kusan makonni biyar ba a nuna an ceto Sumayya daga hannun waɗanda suka yi garkuwa da ita ba.

Sannan kuma Abubuwan da za a iya cewa sun bata wa masu kallon shirin rai su ne: mutuwar Mahmud, yin garkuwa da Sumayya da kuma kasa ceto ta.

Labarai24  ta ci karo da wasu wallafe-wallafe da ma’abota kallon shirin suka yi a shafukan sada zumunta- wallafe-wallafen da suke nuna suka da kuma ƙosawa da kallon shirin.

Ga kadan daga cikin wadan da suka yi korafi akan shirin Labarina.

Arewa Queen tace: Dabara ta ƙarewa marubuta shirin Labarina. Ina jin wannan mutumin shi ne ya haifi duk wani matashi a shirin banda Presido.

Safiyanu Z Yusuf Danman cewa ya yi: Malam Aminu Saira yana shirin zubar da kimarsa. A baya ya kasance ɗaya daga cikin daraktoci mafiya hikima da tunani. Amma bisa yadda yake wasa da hankalinmu, na fara dawowa daga rakiyarsa. Ya kamata waɗanda suke kusa da shi su jawo hankalinsa kafin ya ɓata.

Nura I. Sodangi yace: Wallahi sun yi muguwar kwafsawa. I was telling a friend lokacin da abubuwa suka ƙare ma Mahmud, lokacin da ya yi asarar Laila da ita Sumayya ɗin da kuma ganowar cewa shi shege ne, to a kulle labarinsa da na su laila ɗin. Sai a ɗauko wani sabon labarin cakwakiya da ita Sumayya za ta faɗa. Ba laifi a ci gaba da tafiya da ‘yan kaɗan kamar su Presido da Lukman jifa-jifa.

Amma sam sai na ga wai sun zarce da su Mahmud ɗin. Sai na ce wallahi za su carke.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button