Jarumar shirin Dadin Kowa Adama Matar Kamaye ta bayyana alajar dake tsakanin ta da Sheikh Isah Ali Fantami
Jaruma Zahra’u Saleh wacce aka fi sani da Adaman Kamaye a shiri mai dogon zango na Dadin Kowa wanda tashar Arewa24 take haskawa, bayyana alakar da ke tsakaninta da ministan sadarwa Sheikh Ali Isa Pantami a wata tattaunawa da jaridar Aminiya ta yi da ita.
Kamar yadda Adama ta bayyana cewa, ita ‘yar asalin Jihar Gombe ce kuma ta yi karatun firamare da sakandare a Gombe.
Sannan ta bayyana cewa, Duk wanda aka ji sunansa akwai Pantami dan gidansu ne kuma Sheikh Isa Ali Pantami kanin mahaifinta ne.
A cewarta ta shiga harkar fin ne ta uwar dakinta Hajiya Zulai Bebeji saboda sun zauna tare a Saudiyya don haka bayan sun dawo ta bayyana mata burinta na shiga fim.
Bayan haka ta bayyana yadda ta hada ta da Musa Mai Sana’a wanda ya sa ta a fim dinsa mai suna Hisabi, daga nan ta shiga shirin fim din sosai bayan marigayi Sani SK da Alasan Kwalle sun zama mata tsayayyu biyu a industiri.
Adama ta bayyana yadda taje tantancewar shiga shirin fim din Dadin Kowa na tashar Arewa24 wanda tace sun fi mutane 70 amma taci nasarar zama zakakurar da aka zaba.
Sannan kuma ta bayyana alakar dake tsakaninta da Kamaye inda tace, mutunci ne kawai kuma yana mata gyara idan ya ga ta yi kuskure amma babu wata alakar soyayya a tsakaninsu.
Sannan kuma ta bayyana cewa: A shirye ta ke da tayi aure idan har ta samu mijin da take so kuma dayake lamarin aure sai mutum ya tantance ya kula da kyau.
Ta yi fashin baki dangane da hotunanta da suka bayyana a kafar sada zumunta tare da wani yaro inda tace ba aure su ka yi ba, hotuna su ka dauka na wani fim mai suna ‘Matar Yaro.
Ta kuma bukaci masoyanta da su dinga fada mata gaskiya idan sun ga ta yi kuskure kuma a dinga yi wa ‘yan fim uzuri.
Hakane yayi kyau ldan mutum yayi kuskure Kuma ya nuna yanason gyarawa, to sai a gyaramasa