Labaran Kannywood
Ya kamata Gwamnatin tarayyar Nageriya ta hana yin amfani da manhajar TikTok tun kamin lokaci ya kure, cewar Nazir Sarkin Waka
Ficaccan Mawaki Nazir M Ahmad wanda aka fi sami da Sarkin waka ya yi kira ga Gwamnatin tarayyar Nageriya data hana yin amfani da manhajar Tiktok tun kafin lokaci ya kure.
Advertising
Nazir Sakin Waka ya fadi hakane a wani rubutu daya wallafa a shafin sa na sada zumunta Facebook inda take cewa, Ya kamata gwamnati ta dakatar da TikTok a Najeriya tun kafin lokaci ya ƙure.
A kasan wannan wallafar rubutun da Sarkin waka yayi kimanin mutane 657 ne suka bayyana ra’ayinsu a ƙarƙashin wannan wallafa da Sarkin Waƙa ya yi, inda wasu suke goyon bayan sa wasu kuma suke sukar sa.
Mutane da dama dai a Najeriya suna da ra’ayin mahukunta su toshe manhajar TikTok sakamakon yadda wasu ‘yan mata ke amfani da ita ba ta yadda ya dace ba.
Advertising
Advertising