Uncategory

Umar na shirin Labarina tare da Lukman dakuma Adama Dadin kowa sun sami kyautar gwarzon shekara na 2021

Kamar yadda kuka sani Lukman da kuma Umar sun taka rawar gani a cikin shirin Labarina wanda a yanzu haka aka basu kyautar gwarzon shekara wato, Best Emotional actor of the year.

Wata kungiya dake Jigar Bauchi mai suna Arewa Legend Bauchi sun bada kyautar gwarazan Jarumai a wannan shekarar ta 2021, wanda duk Jaruman da aka basu wannan kyautar sun taka rawar gani matuka.

Luknam ya taka rawar gani sosai a cikin shirin Labarina duba da yadda ya nuna damuwar sa akan batan Sumayya wanda yafi kowa damuwa idan aka dauke mahaifiyar ta, shi yasa ya sami kyautar Best Emotional actor of the year.

Sannan kuma Lukman ya nuna jin dadin sa ga Darakran shirin Malam Aminu Saira akan wannan kyautar da ya samu da kuma role din daya dora shi a kai.

Sai kuma Umar wanda shima yayi nasaar nashe wannan kyautar ta Best Emotional actor of the year, wanda shima ya bada gudun mawar sa wajan jajircewar sa akan role din da aka dora shi.

Sai kuma Adama wanda ake mata lakabi da Matar Kamaye ita ma ta sami wannan kyautar duba da yadda ake taka rawar gani a cikin shirin Dadin Kowa mai dogin zango wanda tashar Arewa24 take haskawa.

Ga hotunan nasu a kasa domin ku kalla.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button