Labaran Kannywood
Adam A Zango ya koka kan masu damfara mutane da sunan sa.
Fitaccen jarumi a masana’antar Kannywood Adam A Zango ya koka kan masu damfarar mutane da sunan sa a shafin Facebook.
Jarumin yace yana karbar zagi da cin mutunci a waje jama’a da suke damfara naira dubu goma wasu dubu biyar. Jarumin ya kuma ce ya rasa wane irin dakikanci ne yake damun mutane duk wakar sa sai ya fada bashi bane bashi bane amma sunki su gane.
magana aka ce bakin mai ita tafi dadi ga magan ganun da jarumin ya fada akan wannan mutane.