Labarai

A karon farko Shatu Garko sarauniyar kyau tayi magana akan abubuwan da take fuskanta bayan ta lashe gasar sarauniyar kyau a Nageriya

Tun bayan da Musulma kuma bahaushiya Shatu Garko tayi nasarar lashe kambun gasar sarauniyar kyau na kasa ake ta maganganu daban-daban akan lamarin, wanda har hukumar Hisbah ta sha alwashin kiran iyayan Shatu Garko domin a fadakar su kan illar abin da tayi wanda hakan ya kara tada kurar lamarin.

Mutane sun yi kaso biyu kan lamarin inda mutane farko suke goyon bayan Hisbah da sauran Malaman addini dake ganin shiga gasar sarauniyar kyau haramun ne, kuma abin Allah wadai ne ace Musulma ta shiga wannan abu na tallata sura da tsiraici da suna sarauniyar kyau.

Sai kuma daya tsagin mutanen suke ganin wannan wani cigaba ne ace ana wani abu a kasa sau 43 ba’a taba samin wanda ya lashe daga yankin Arewa ba sa a wannan karon, kuma abin alfahari ne wacce ta lashe din bata bayyana surar ta ba.

Sannan tasa dankwalinta abin duk da masu fafatawa a gasar basu saba ta kuma rufe ko’ina a nikin ta, sai dai kayan da tasa ne sun matse ta.

Wanda suke ganin wannan abin alfahari ne ace Musulma mai shigar Musulinci taci nasara akan masu bayyana tsiraici wanda a ganin su goya mata baya da alfarma da nasara da tayi ta hanyar rufe jikin.

Zai karfafa gwairwar ‘yam matam mu masu son koyi da arnan chan masu bayyana tsiraici su san koda sun bi tsarin suturar jiki kamat yadda addini ya tanadar, zasu iya nasara ako menene ba sai sun bayyana tsiraicin su ba.

Ku kalli bidiyon dake kasa domin kuji maganar da Shatu Garko tayi a lokacin da suka yi shira da BBC Pidgin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button