Advertising
Advertising
Labarai

Jarumar Nollywood wacce tasha yin zina da Mutane a kwanakin baya ta bayyana cewa bazata sake yin Jima’i ba sai tayi Aure

Ficacciyar Jarumar Fina-Finai ta Kudancin Nageriya Nollywood mai suna “Sylvia Ukaatu” ta yi alkawarin bazata sake yin Jima’i ta hanyar da ba aure ba, domin a yanzu ta koma ga Allah.

Advertising

“Sylvia Ukaatu” ta bayyana hakan ne a wata shira da aka yi da ita inda taci alwashin daukar wannan alkawarin na cewa indai har ta sake yin Jima’i da wani to tabbas aure suka yi.

Inda tayi nadamar abubuwan da ta aikata a shekarun baya wanda shaidan ya rinjaye ta, wanda yanzu kuma ta shiya yin tuba sannan kuma zata koma ga Allah domin daina aikata abunuwan da tayi a shekarun baya.

Sannan Sylvia Ukaatu ta bayyana cewa: Na koma ga Allah Ba zan sake fifita kudi kan tsoron Allah ba Dukkan shekarun nan ba tare da biyayya ga Allah ba sun zama aikin banza, shi yasa nayi alkawarin cewa ba zan sake jima’i ba sai na yi aure.

Advertising

Ina addu’a wannan sabon matsaya da na dauka zai wanke min zunubai na lokacin da nike bin shaidan.

Ta kara da cewa: Na kasance mai son jima’i sosai kuma na yi zinace-zinace saboda lokacin rayuwata nake ci, Lokaci ya yi da zan koma ga mahalicci na. Idan lokaci yayi zai bani masoyi na.

Jaruma Sylvia Ukaatu Yar jihar Anambra ce wacce a baya ta bayyana yadda take son jima’i sosai, baya haka kuma ta yi zina da mutane daban-daban a wancan lokacin.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button