Advertising
Advertising
Labarai

Subahanallah: Yadda halin yan gudun hijira a Jihar Zamfara suke cikin kuncin rayuwa

HALIN DA ZAM FARA TAKE CIKI A YAU. Audu Bulama Bukarti.

Advertising

A matsayinka na daya daga cikin mahukunta wannan jaha.

  • Shin a wannan hali kana iya barci kuwa?
  • Shin kana iya murmushi har da dariya?
  • Kana amfani da kudin wannan jaha wajen biyan naka bukatu da iyalinka.

A haka yadda ake tafiya a naka tunani babu wata matsala ko wani sakamako ko alhaki da zai biyo baya?, Kana tsammanin shi ke nan za’a cigaba da tafiya a haka kuma kai ka zauna lafiya kai da iyalanka babu wani hukunci, jarabawa musiba ko biyan bashin alhaki daga Ubangiji? Anya?.

Yau Jabir Mustapha Sambo na BBC Hausa ya kai ziyara kuma yayi hira da ‘yan gudun hijira na Jihar Zamfara, Wallahi babu mai imanin da zai ji halin da matan nan suke ciki hankalinsa bai tashi ba idon shi bai cika da hawaye ba.

Advertising

Matan da ‘yan bindiga suka sace suka ci zarafin su tsawon lokaci yanzu ba su da abinci sai dai suci tafasa kullum, sannan akwai matar da ruwan surfe suke sha su rayu da ‘yayan ta yara kanana suna fa da yunwa da rashin lafiya Ba su da gurin kwana mai kyau, balle ruwan sha.

Muna kira ga Buhari da Matawalle da suyi gaggawar kafa wa wadannan mata sannanin ‘yan gudun hijira domin su samu gurin kwana da abinc, Wallahi Buhari da Gwamna Matawalle ku ji tsoron Allah Ranar kiyama Allah zai titsiye ku akan hakkin wadannan bayin nasa.

Jama’a mu ji tsoron Allah idan mahukunta sun ki sauke nauyinsu lalle ne mu sai mu tashi muyi iya-iyawarmu, Wadannan ‘yan uwanmu ne kuma suna da hakki akanmu wannan rashin imani yayi isa haka muji tsoron Allah.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button