Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bayyana cewa Sheikh Dr Ibrahim Jalo Jalingo Dan Wiwi ne
Shugaban Majalisar Malaman kungiyar Izala ta Duniya Ash-sheikh Muhammad Sani Alhaji Yahya Jingir (H) ya kwatanta Babban Malamin addini Sheikh Dr Ibrahim Jalo Jalingo (H) a matsyain ‘Dan wiwi, sabida fahimtar da yake yadawa akan makomar iyayen Annabi (SAW).
Sheikh Sani Yahaya Jingir fadi cewa, Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo dan wiwi ne wanda bai san mutuncin kansa balle ya san mutuncin wani, yana hada husuma da raba kan Musulmai inji Dattijon Malami Sheikh Sani Yahya Jingir.
Abu na farko banji dadi da Sheikh Sani Yahya Jingir ya fito ya bayyana wa duniya cewa Sheikh Dr Ibrahim Jalo Jalingo Dan Wiwi ne, hakan bai kamata ba ko da ya tabbata Malamin yana shan wiwi.
Abu na biyu Sheikh Dr Ibrahim Jalo mutumin kirki ne wanda ya sadaukar da rayuwarsa akan yada addinin Allah, sannan baya jin tsoro ko shakkar mayar da raddi ga kafurai da wadanda suke yakar Musulunci, sannan Malami ne mai tsananin gudun duniya.
Ga cikekkiyar bidiyon a kasa domin ku kalla.