Wasu Jaruman Kannywood Mata sun dawo harkar Fim bayan shekarun da suka dauka ba tare da ana ganin su ba
Wasu daga cikin Jaruman Masana’antar kannywood wanda suka bar harkar tun bayan da suka yi aure tsaron shekaru goma sha uku 13, to a yanzu Jaruman sun dawo Masana’antar Kannywood domin su cigaba da harkar Fim kamar yadda suka yi a baya.
Maryam Abubakar Jan Kunne tsohuwar budurwar Sani Danja wanda ba su kai ga aure ba, ta auri wani daban.
Fati Muhammad tsohuwar matar Sani Musa Mai Iska kuma tsohuwar matar Umar Kanu, yayan Ali Jita.
Amina Uba Hassan tsohuwar matar Adam A. Zango ta farko, kuma Maman ɗan sa Haidar.
Duk wadan nan Jaruman guda uku 3 wanda muka kawo sun yi aure ne tun bayan shekaru goma sha uku 13 da suka gabata, inda wasu daga cikin su ma tsawon shekarun da suka dauka basa harkar Fim sun fi 13.
To sai a wannan karon kuma tsofaffin Jaruman suka dawo Masana’antar Kannywood domin su cigaba da harkar Fim dim.